-- <b>Tubalin aiki don amfani lokacin fara afilikeshon daga layin umurni</b>

<big>L</big>okacin farawa da tubalin aiki <tt>-v</tt> ko <tt>--version</tt>, ana nuna siga na yanzu na Kickshaw. Tubalin aikin <tt>-h</tt> da <tt>--help</tt> suna amfani don gabatar da bayani akan yadda za a sami tagar shawarwari, sai jerin tubalin aiki da ake karɓa.
Ana iya fara Kickshaw kuma da hanyar fayil zuwa mazaɓa a matsayin tubalin aiki. Sakamakon ƙari na wannan shine, ya sa yana yiwuwa a buɗe fayilolin mazaɓa da Kickshaw ta hanyar amfani da mazaɓar mahalli a cikin sarrafa fayiloli.

-- <b>Fayilolin da Kickshaw ke ƙirƙira</b>

<b>Na har abada</b>

Kickshaw yana ƙirƙirar fayil ɗin saiti nasa da sunan <tt>.kickshawrc</tt>, wanda yake a cikin ma'ajiyar gida na mai anfani da kwamfuta.

<b>Na ɗan lokaci</b>

Don kowane gyara da aka yi, ana ƙirƙirar fayil na tarin maida baya a cikin <tt>/tmp/kickshaw.XXXXXX</tt> (alamomin X wurin ajiye ne don haruffa da lambobi na bazuwa). Idan an dakatar da shirin ba da gangan ba, folda zai daɗe, amma wannan bai kamata ya haifar da damuwa ba tun da yana dauke da ƙananan fayiloli kawai kuma yawanci za a goge shi ta atomatik kawai a ƙarshe lokacin sake kunnawa na gaba.

Kickshaw yana ƙirƙirar fayil na OtoAdana a cikin folda na gida da sunan <tt>.kickshaw_autosave</tt>. Ana sabuntawa shi bayan kowane gyara kuma ana gogewa shi lokacin da aka rufe shirin. Idan an dakatar da Kickshaw ba bisa tsari ba, lokacin fara shirin na gaba, ana tambayi mai anfani da kwamfuta ko ya mayar da mazaɓa daga OtoAdana ko ya goge fayil ɗin OtoAdana.
